Za’a Sake Bude Filayen Jirgin Sama


Ministan sufurin jiragen sama, na kasa Hadi Sirika,  ya ce matafiyi ne kawai za a ba su dammar shiga cikin tashar jirgin saman. Ya sanar da hakan ne a ranar Laraba cewa filayen jirgin saman Abuja da Legas za su ci gaba da ayyukan cikin gida a ranar 8 ga Yuli; da filayen jirgin saman Kano, Fatakwal, Owerri da Maiduguri, 11 ga Yuli.
Sirika, a cikin wata tattaunawar suka yi da mambobin kwamitin Majalisar Dattawa kan Haya a Abuja, ya ce: “Duk wadanda ba su da harkokin kasuwanci tabbas ba za a basu izinin shiga tashar jirgin saman ba. Ya ce an sanya injina da ke aiwatar da fasinjoji cikin sauri a filayen jirgin saman.

Sirika ya ce ma’aikatar sa tana aiki tare da kamfanonin jiragen sama don bullo da ka’idoji kafin su sake budewa.Comments


Post Your CommentLocal News

Foreign News


© 2020 Copyright: visionfm.ng