SHUGABA BUHARI YA YABA DA KARFIN DANGANTAKA DAKE TSAKANIN NAJERIYA DA KASAN PAKISTAN


Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranan alhamis ya nuna farin cikin sa bisa irin karfin alakan dake tsakanin najeriya da Pakistan wanda yace wannan yanayin ya dauki tsawon lokaci na alaka tsakanin soji da soji an kulla alaka.
Da ya ke jawabi a wani tattaunawan bankwana tare da Mejo Janar Waqar mai (murabus) babban kwamishina mai barin gado na kasar Pakistan a najeriya, Shugaba Buhari ya kwatanta dangantakan da ke tsakanin najeriya da Pakistan a matsayin mai kyau kuma mai nisa-kai ga duba baya na tsawon lokaci a tarihi.
Shugaban kasa yace idan ka ware bangare guda na aikin soji da hadin gwiwa tsakanin kasashen guda biyu a matsayin yardaddiya wanda ake amfana.
“bugu da kari da kuma kokarin kasashen guda biyu a cikin kasashen Commonwealth sojojin kasar Pakistan sun horar da sojojin najeriya yana da muhimmanci. wannan dangantaka na alaka yana da tarihin tsawon lokaci da nisa, ina tunawa da cewa abokan aiki na marigayi Janar Shehu Yar’adua da kuma Mai Martaba Sarkin Gwandu na yanzu Muhammadu Bashir, tsofin janar janar dukkanin su sun samu horo a kasar Pakistan,” inji shi .
Shugaban kasa haka kuma ya yaba ma Wakilin kasar mai barin gado na kara karfafa dangantaka na kasashen musamman a bangaren tattalin arziki da hadin kai.
A nasa mai da jawabi, jakadan Kingravi yayi godiya ma Shugaban kasa Buhari da kuma mutanen najeriya wanda ya kwatanta a matsayin mai karban baki na mai hayayyafa, jindadi, kuma samun ilimi a ziyarce ziyarcen sa a Najeriya.”
Yayi alkawarin bada goyon bayan kasan sa a shirye shiryen samar da tsaro da goyon baya da hadin kai na soji domun fada da masu tayar da kayan baya da kuma gabatarwa da dukkanin mataloli da sanadi ma kasan sa.”Comments


Post Your CommentLocal News

Foreign News


© 2020 Copyright: visionfm.ng