;
Manyan shugabanni daga kungiyar tsaro ta Tarayyar Turai, sun yi Allah-wadarai da shirin gudanar da kuri'ar raba gardama da za a yi a yankunan da Ukraine da Rasha ta mamaye

Manyan shugabanni daga kungiyar tsaro ta Tarayyar Turai, sun yi Allah-wadarai da shirin gudanar da kuri'ar raba gardama da za a yi a yankunan da Ukraine da Rasha ta mamaye

Manyan shugabanni daga kungiyar tsaro ta Tarayyar Turai, sun yi Allah-wadarai da shirin gudanar da kuria’r raba gardama da za a yi a yankunan da Ukraine da Rasha ta mamaye.

A wata sanarwa ta hadin guiwa daga ofishin shugaban na ministan harkokin wajen Poland Zbigniew Rau, da Babbar Sakatariya Helga Maria Schmid da kuma sauran jami’an diflomsaiyya suka yi sukan.

Jami’an da ke samun goyon bayan Rasha a yankunan Ukrine da Rasha ke iko da su sun ce suna son yin kuriar raba gardama kan shiga Rasha, wadda za su fara daga wannan makon.

Sanarwar wadda ta fito daga hukumar tsaron ta Tarayyar Turai ta ce kuri’ar raba gardamar da aka shirya yi ta saba wa doka.

Sanarwar ta ce hukumomin da suke da halarci na doka ne kawai za su iya shirya wannan kuri’a bisa tanadin dokokin kasa.

Hukumar ta ce yayin da yaki ke ci gaba da gudana duk wata kuria’r raba gardama da wadanda suka mamaye yankunan Ukraine za su yi, abu ne da ya sabawa dokokin duniya.