;
Sanatoci sun yi wa Buhari rubdugu kan rashin tsaro

Sanatoci sun yi wa Buhari rubdugu kan rashin tsaro

Kwana daya bayan komawarsu daga hutun shekara, ‘yan majalisar dattawan Najeriya sun yi kira ga gwamnatin Shugaba Buhari da ta sauya salon tafiyar da sha’anin tsaro a kasar.

Dan majalisar dattawa mai wakiltar arewacin jihar Kebbi, Sanata Abdullahi Yahaya Abubakar ne dai ya mika bukatar yi wa tsarin tsaron kasar garanbawul ga zauren majalisar a zamanta na ranar Laraba.

Yayin gabatar da bukatar tasa mai taken ‘Matsalolin tsaro a Najeriya: Bukatar gaggawa domin yi wa tsarin tsaron kasa kwaskwarima’, ga zauren majalisar, Sanata Abdullahi Yahaya Abubakar ya ce “dole a tashi tsaye domin tunkarar matsalar tsaro da ke addabar sassan kasar baki daya.

Wannan bukata ta Sanata Abdullahi Yahaya Abubakar ta samu karbuwa a zauren majalisar, inda sanatoci 105 daga cikin 109 suka yi na’am da bukatar.

Hakan ne ya sa ‘yan majalisar ta dattawa daya bayan daya suka yi ta tofa albarkacin bakinsu kamar haka;

Sanata Abdullahi Adamu mai wakiltar jihar Nassarawa cewa ya yi “idan har ba mu yi wa wannan batun adalci ba to za mu kasance mun lalata tsarin tsaron kasar maimakon mu gyara.”Shugaban marasa rinjaye na majalisar, Sanata Abaribe ya bukaci Shugaba Buhari ya yi murabus daga kujerar shugabancin kasar bisa zargin gaza samar da tsaro ga ‘yan kasa.

Shi ma Sanata Adamu Aliero mai wakiltar jihar Kebbi ya ce “‘yan sandan kasar sun yi kadan bisa la’akari da yadda aiki ya yi musu yawa a saboda haka ya kamata a dauki sabbin ‘yan sanda kusan milyan daya.”A nasa bangaren, Sanata George Sekibo ya ce “akwai bukatar komawa a tuba ga Ubangiji sannan a dauki sabon salon tunkarar matsalar tsaro….”Shi kuwa tsohon gwamnan jihar Ogun, Sanata Ibikunle Amosun ya ce kamata “ya yi kowacce jiha ta samar da ‘yan sandanta idan dai har ana son ‘yan dokar su samar da tsaro mai inganci…”